Paulo Fonseca ya yi maraba da daukar Mourinho aikin horar da Roma
Wallafawa ranar:
Manajan kungiyar kwallon kafa ta Roma, Paulo Fonseca ya yi maraba da matakin daukar Jose Maurinho matsayin mai horar da kungiyar da ke doka gasar Serie A ta Italiya.
Maurinho dai zai maye gurbin Fonseca a karshen kaka wajen jan ragamar kungiyar yayinda tuni ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru 3, kwanaki kalilan bayan korar da Tottenham ta yi masa watanni 17 bayan fara aikin horar da tawagarta.
Bayan matakin korarsa daga kungiyoyin kwallon kafa na Manchester United da kuma Chelsea da ma Tottenham a baya-bayan nan, Mourinho da Duniya ke kallo a matsayin babban manaja a fagen horar da tamaula, za a iya cewa tauraruwarsa na neman dusashewa.
A cewar Paulo Fonseca, ko shakka babu Mourinho zai yi rawar gani wajen kafa tarihi a kungiyar kasancewarsa fasihin Koci da ya kware wajen dage kofunan gasar Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu