Tuchel ya kafa sabon tarihi a gasar Zakarun Turai
Wallafawa ranar:
Thomas Tuchel ya kafa tarihin zama koci na farko da ya samu nasarar kaiwa wasan karshe na gasar zakarun turai sau biyu a jere tare da kungiyoyi daban daban.
Tuchel ya kafa tarihin ne bayan jagorantar Chelsea wajen lallasa Real Madrid da jumillar kwallaye 3-1 a wasanni biyun da suka fafata a zagayen wasan kusa da na karshe Semi Final, inda a zangon farko suka tashi kunnen doki 1-1, a jiya Laraba kuma kungiyar ta Chelsea ta lallasa Real Madrid da 2-0.
A shekarar da ta gabata, kocin na Chelsea Thomas Tuchel ne ya jagoranci PSG zuwa wasan karshe na gasar ta Zakarun Turai, inda yayi rashin nasara a hannun Bayern Munich da 1-0.
A bana kuma Tuchel zai jagoranci Chelsea wajen fafatawa da Manchester City kan kofin gasar ta zakarun Turai, wasan da za a fafata a ranar 29 ga watan Mayu da muke ciki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu