Wasanni-Kwallon Kafa

Farin jinin Arsenal na dusashewa saboda rashin katabus a bana

'Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal.
'Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal. Julian Finney POOL/AFP/Archives

Ga alama farin jinin kungiyar Arsenal da ke wasa a gasar Firimiya ta Ingila na cigaba da dakushewa sakamakon rashin nasarorin da take samu da kuma kasa katabus a gasar wasanni 4 da ta shiga bana amma ta kasa kai labari.

Talla

Shan kashin da kungiyar tayi daga kungiyar Villareal wadda ta fitar da ita daga gasar cin kofin Europa bayan karawar da suka yi sau biyu ya kawo karshen duk wata fata na lashe kofi da kungiyar ke da ita.

Bayan nasarar da Villareal ta samu akan Arsenal a makon jiya da ci 2-1, kungiyar da tsohon manajan Arsenal Unai Emery ke koyarwa ta bita har London inda suka tashi ba tare da wata kungiya ta samu nasara ba, abinda ya sa ta fitar da Arsenal daga gasar baki daya.

Dama kuma wannan shine kofi daya tilo da ake saran Arsenal zata taka rawar ganin saboda yadda aka cire ta a gasar FA da Carabao, yayin da take matsayi na 9 a teburin Firimiya.

Wadannan rashin nasarori ya sa kungiyar ta koma na ‘yan baya ga dangi wajen rasa kimar ta da kuma hana ta samun damar karawa a nahiyar Turai a kaka mai zuwa saboda gazawar ta na zama cikin kungiyoyi 6 na farko a teburin Firimiya.

Manajan kungiyar Mikel Arteta yace sun yi iya bakin kokarin su wajen ganin sun samu nasara amma kokarin na su bai isa ba, kuma kowanne daga cikin su na da alhakin yanayin da kungiyar ta samu kan ta.

Tuni wasu tsoffin Yan wasan kungiyar suka fara bayyana ra’ayoyin su wajen ganin anyi gyara kan yadda ake tafiyar da ita wajen kashe kudi domin saya mata ‘yan wasan da suka dace da zasu dawo da kimar ta a gasar Firimiya da kuma Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI