Wasanni

Hazard ya nemi yafiyar magoya bayan Real Madrid kan wasansu da Chelsea

Dan wasan gaba na Real Madrid, Eden Hazard yayin karawarsu da tsohuwar kungiyarsa Chelsea.
Dan wasan gaba na Real Madrid, Eden Hazard yayin karawarsu da tsohuwar kungiyarsa Chelsea. UEFA via Getty Images - Steve Bardens - UEFA

Dan wasan gaba na Real Madrid Eden Hazard ya nemi yafiyar magoya baya, kan dariya da sowar da ya rika yi da tsaffin abokanan wasansa na Chelsea bayan kammala karawarsu ta shekaran jiya da Chelsea ta yi waje da Madrid daga gasar cin kofin zakarun Turai bayan ratata mata kwallaye 2 da nema.

Talla

Hazard tsohon dan wasan Chelsea mai shekearu 30 da ya koma Real Madrid a 2019 ya gamu da caccakar magoya baya har ma da jaridun Spain kan yadda aka rika hasko shi yana nishadi da ‘yan wasan na Chelsea ba tare da jin zafin ciresu da kungiyar ta yi ba.

Sai dai tuni Hazard ya nemi yafiyar magoya bayan Real Madrid a sakon da ya wallafa a shafinsa na Intagram inda ya ce bai yi hakan da nufin bakanta musu ba, face sabon da ke tsakaninsa da tsohuwar tawagar ta sa.

Eden Hazard wanda aka sauya shi gabanin karkare wasan na ranar Laraba saboda rashin abin kirkin da ya yi a wasan, kiraye-kirayen ganin Madrid ta sayar da shi ya tsanata bayan wasan wanda Kungiyar ta Spain ta sha kaye, zuwa yanzu kwallaye 4 ya iya zurawa a wasanni 40 da ya dokawa Real Madrid .

Yayin taka ledarsa a Chelsea, Hazard ya taimakawa tawagar ta sa dage kofunan firimiya 2 na Europa 2 yayinda ya zura kwallaye fiye da 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI