Wasanni-Kwallon Kafa-Neymar

Neymar ya sanya hannu a sabon kwantiragi da PSG zuwa 2025

Dan wasan PSG da Brazil, Neymar Jr.
Dan wasan PSG da Brazil, Neymar Jr. FRANCK FIFE AFP

Tauraron ‘dan wasan Brazil Neymar Junior ya sanya hannu a kan wata sabuwar kwangilar da za ta kai shi zama a kungiyar PSG har zuwa shekarar 2025.

Talla

Neymar yace kwanciyar hankali da kuma farin ciki ya sa shi rattaba hannu akan sabuwar kwangilar domin tsawaita zaman sa a birnin Paris dake kasar Faransa.

‘Dan wasan gaban ya koma kungiyar PSG ne a shekarar 2017 lokacin da kungiyar ta biya Fam miliyan 200 domin sayo shi a ciniki mafi tsada da aka taba gani a harkar kwallon kafa.

An dade ana danganta Neymar da komawa tsohuwar kungiyar sa ta Barcelona, amma ’dan wasan ya ce ya dada girma a matsayin sa na dan kwallo da kuma Bil Adama, kuma ya san ciwon kan sa.

Neymar ya jefawa PSG kwallaye 85 tun bayan komawar sa kungiyar da kuma taimakawa wasu jefa 51 a wasanni 112 da ya bugawa kungiyar duk da fama da raunukan da yayi a wasu lokuta.

A wasu lokuta ya fuskanci matsaloli tsakanin sa da magoya bayan kungiyar saboda rade radin cewar yana shirin komawa kungiyar Barcelona abin da ya sa wani lokaci su kan masa ihu.

Sai dai ‘dan wasan yace ya koyi darasi da dama, domin wasu abubuwa sun faru da shi wadanda bai dace ace sun faru ba, amma duk da haka yana farin cikin cigaba da zaman sa a kungiya.

Neymar ya bayyana fatarsa na ganin ya lashe kofuna da dama a kungiyar PSG, bayan lashe kofuna guda 3 da yayi na gasar Ligue 1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI