Birtaniya - Turkiya

Birtaniya ta gargadi magoya bayan City kan zuwa Turkiya

Magoya bayan Manchester City.
Magoya bayan Manchester City. AP - Matt Dunham

Gwamnatin Birtaniya ta gargadi magoya bayan kungiyar manchester City da Chelsea da su kaucewa tafiya Turkiya domin halartar wasan karshe na cin kofin zakarun Turai da za’ayi ranar 29 ga wannan wata saboda cutar korona.

Talla

Sakataren sufurin kasar Grant Shapps yace matakin ya biyo bayan sanya Turkiyar cikin jerin kasashen dake fama da yaduwar cutar, yayin da ya kuma ce a shirye suke su dauki nauyin wasan karshen idan hukumar UEFA ta bayyana shirin dauke was an daga Santanbul.

Shapps yace suna tattaunawa da hukumar domin janyo hankalin ta da ta dauke wasan daga Turkiya saboda yadda cutar koronar ke mata barazana.

Sakataren yace Birtaniya tayi suna wajen daukar manyan wasanni tare da karbar Yan kallo, saboda haka a shirye suke su karbi wasan idan an basu izini.

Hukumar UEFA ta baiwa kowacce kungiya daga cikin kungiyoyin Chelsea da Manchester City tikiti 4,000 domin halartar wasan karshen da za’ayi a tsakanin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI