Wasanni - Spain

Fatan Real Madrid na karbe jagorancin La Liga ya gamu da cikas

'Yan wasan Real Madrid da Sevilla yayin fafatawar da suka tashi 2-2 a gasar La Liga. 09/05/2021.
'Yan wasan Real Madrid da Sevilla yayin fafatawar da suka tashi 2-2 a gasar La Liga. 09/05/2021. © Susana Vera/ Reuters

Fatan kungiyar Real Madrid na darewa kan gaba a gasar La Liga ya gamu da cikas bayan da ta tashi 2-2 da kyar a wasan da suka fafata da Sevilla ranar Lahadi a birnin Madrid.

Talla

Marco Asensio da Eden Hazard ne suka ciwa Madrid kwallayen ta, a yayin da Sevilla ta samu nata daga Fernando da kuma Ivan Rakitic, tsohon dan wasan Barcelona.

Kaftin din Barcelona Lionel Messi tare da dan wasan Atletico Madrid Luis Suarez a yayin wasan da suka tashi 0-0 a gasar La Liga.
Kaftin din Barcelona Lionel Messi tare da dan wasan Atletico Madrid Luis Suarez a yayin wasan da suka tashi 0-0 a gasar La Liga. © REUTERS

Kafin wasan na Sevilla da Real Madrid a jiya Lahadi, manyan abokan hamayyarsu wato Barcelona da Atletico Madrid ne suka soma karawa, inda wasa ya tashi canjaras 0-0.

Har yanzu dai ba san maci tuwo ba sai miya ta kare a gasar La Ligar ta Spain, domin a halin yanzu Atletico Madrid ke kan gaba da maki 77, Real Madrid na biye da maki 75, sai Barcelona ta uku itama da makin 75, yayin da Sevilla ke da 71 a matsayi na 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI