Wasanni - Italiya

Seria A: Juventus ka iya rasa gurbi a tsakanin kungiyoyi 4 na farko

Tauraron Juventus Cristiano Ronaldo.
Tauraron Juventus Cristiano Ronaldo. © Marco Bertorello/AFP/Getty Images

AC Milan ta wargaza lissafin kungiyar Juventus dake fatan kammala gasar Seria A ta bana a tsakanin kungiyoyi 4 na farko, bayan fafatawar da suka yi a daren ranar Lahadi.

Talla

Yayin wasan dai AC Milan ta lallasa Juventus ne da kwallaye 3-0, ta hannun ‘yan wasanta Brahim Diaz, Fikayo Tomori, da kuma Anton Rebic.

Yanzu haka Juventus ta koma matsayi na 5 da maki 69, maki 1 tsakaninta da Napoli dake matsayi na 4, yayin da ya rage wasanni 3 a buga domin karkare wasannin gasar Seria A na bana.

Sai dai masana na ganin akwai jan aiki gaban Juventus kafin ta sake komawa cikin kungiyoyi 4 na farko, la’akari da cewar dole ta samu nasara kan Inter Milan da tuni ta lashe kofin Seria A na bana, yayin karawar da za su a karshen mako mai zuwa.

Yanzu haka dai Inter Milan da ta dage kofi na da maki 85, Atalanta na biye da maki 72, AC Milan ta 3 itama da maki 72, yayin da Napoli ke da maki 70 a matsayi na 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI