Wasanni - Najeriya

Ahmed Musa zai haska a wasan da Pillars za ta kara da Adamawa United

Dan wasan Najeriya Ahmed Musa da sake komawa tsohuwar kungiyar Kano Pillars a gasar Firimiyar Najeriya.
Dan wasan Najeriya Ahmed Musa da sake komawa tsohuwar kungiyar Kano Pillars a gasar Firimiyar Najeriya. © AP

Kungiyar Kano Pillars tace sabon dan wasanta kuma kaftin din tawagar kwallon kafar Najeriya Ahmed Musa zai buga mata wasan farko tun bayan komen da yayi mata ranar Lahadin nan dake tafe wato 16 ga watan Mayu.

Talla

Musa zai soma haskawa Pillars ne yayin fafatwar da za su yi da Adamawa United a gasar Firimiyar Najeriya.

Was ana baya bayan nan da Pillars ta fafata da Warri Wolves a birnin Warri an tashi ne kunnen doki wato 1-1.

Bayan buga wasanni 20 a. gasar Firimiyar Najeriya, a halin yanzu  Akwa United ke kan gaba da maki 37, Kano Pillars ta 2 itama da maki 37, sai Kwara United ta 3 da maki 36, yayin da Rivers FC ke da maki 35.

A can kasa kuwa Ifeanyi Ubah ce ta 19 da maki 17, sai Adamawa United ta 20 da maki 12.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI