Wasanni-Kwallon Kafa

Cavani ya tsawaita yarjejeniyarsa da United zuwa 2022

Dan wasan gaba na Manchester United Edinson Cavani.
Dan wasan gaba na Manchester United Edinson Cavani. AP - Jon Super

Dan wasan gaba na Manchester United Edinson Cavani ya rattaba hannu kan tsawaita yarjejeniyarsa da kungiyar da karin shekara guda, wadda za ta kare a watan Yunin shekarar badi ta 2022.

Talla

Dan wasan mai shekaru 34 na cigaba da taka rawar gani a wasannin da United ta fafata a ciki da wajen Ingila a makwannin baya bayan nan, inda ya ci kwallaye takwas, tare da taimakawa wajen cin wasu 3, cikin wasanni 7 da ya buga.

A jumlace kwallaye 15 Cavani ya ciwa Manchester United a dukkaninsu wasannin da ya buga mata na kakar wasa ta bana, 9 daga cikinsu kuma ya jefa su ne a gasar Firimiyar Ingila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI