Wasanni-Kwallon Kafa

Manchester City ta zama zakarar Firimiya ta bana karo na 3 a shekaru 4

Manchester City ta dage kofin na Firimiya sau 5 cikin shekaru 10.
Manchester City ta dage kofin na Firimiya sau 5 cikin shekaru 10. Rui Vieira POOL/AFP

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta zama zakarar Firimiyar Ingila bayan rashin nasarar takwararta Manchester United a hannun Leicester City da kwallo 2 da 1 yau Talata, nasarar da ke zuwa bayan doka wasannin gasar 35. 

Talla

Kungiyar ta Manchester City wadda yanzu haka ke tunkarar wasan karshe na cin kofin zakarun Turai, bayan tun farko ta dage kofin kalubale na Carabao a watan jiya, ta bude wuta a wannan kaka bayan kufcewar kofin na Firimiya a bara.

A kalaman Pep Guardiola gabanin nasarar Leicester kan Manchester United ya bayyana cewa City ta cancanci lashe kofin kowacce gasa a yanzu.

A cewar Guardiola za su dage kofin na Firimiya gaban dubunnan magoya bayansu, bayan matakin gwamnati na baiwa magoya baya shiga filayen wasanni a wasa guda na kowacce kungiya gabanin karkare gasar.

Manchester United dai ta yi rashin nasara da kwallo 1 da 2 ne har gidanta a hannun Leicester wanda ya kara tazarar da ke tsakaninta da City duk da ya ke kungiyar na da kwantan wasa guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI