Wasanni-Kwallon Kafa

Busquets na fargabar Barcelona ba za ta kai labari ba

Maki daya ne tsakanin Barcelona da Atletico madrid.
Maki daya ne tsakanin Barcelona da Atletico madrid. Josep Lago AFP/Archivos

Sergio Busquets ya yi amannar cewar damar kungiyarsa, Barcelona ta lashe gasar La Ligar bana ta gushe bayan da suka buga canjaras 3-3 da Levante a jiya Talata.

Talla

Barcelona na jan ragamar wasan na Talata da kwallaye 2 -0 kafin a tafi hutun rabin lokaci daga Lionel Messi da Pedri, amma sai bakin suka yunkuro suka farke wadannan kwallaye bayan an dawo ta hannun Gonzalo Melero da Jose Luis Morales.

Duk da cewa Ousmane Dembele ya dora Barca a turbar nasara da kwallo ta 3 da ya ci, Sergio Leon ya farke a minti na 83rd.

Wannan sakamako  ya sa Barcelona a bayan masu jan ragamar gasar, kuma ya sa maki daya ne tak tazararsu da abokan hamayyarsu Real Madrid, kuma dukkanninsu na da kwanten wasa daya.

Atletico na iya kara shiga gaban Barcelona a yau Laraba idan suka doke Real Sociedad a wasan da  zasu karbi bakuncinsu.

 Real kuma za su samu damar shigewa gaban Barcelona idan suka yi nasara a ziyarar da za su kai Granada a gobe Alhamis.

Busquets ya ce makin da suka rage ‘yan kalilan ne, kuma, samun nasarar lashe gasar ga kungiyarsa zai ta’allaka ne ga abin da abokan hamayyarsu suka yi a wasanninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI