Wasanni-Kwallon Kafa

City sun lashe kofin Firimiya karo 5 cikin shekaru 10 duk da kalubalen Korona

Manchester City sun zama zakarun gasar Firimiyar Ingila ta bana.
Manchester City sun zama zakarun gasar Firimiyar Ingila ta bana. WOLFGANG RATTAY POOL/AFP

Manchester City sun zama zakarun gasar Firimiyar Ingila a karo na 5 cikin shekaru 10, lamarin da ya jaddada matsayinsu  na wadanda suka mamaye gasar kwallon kafar ta kasar Ingila.

Talla

Wannan ne kofin Firmiya na 3 da Guardiola ya lashe a zamnasa na Man City, a kakar da aka yi wasa a filayen wasan da kusan babu kowa  saboda bullar annobar  coronavirus.

City sun gamu da cikas a makonnin farko na gasar wannan kaka, amma  suka farfado  a tsakiyar watan Disamba, kuma daga nan suka karkare gasar da wasanni 3 a hannu.

Ga mahiman lokatan da suka bai wa City wannan kofi a wannan kaka:

Bayan da Leicester City suka lallasa su da ci 5-2 har gida a wasansu na farko a gida, babu wanda ya yi tunanin cewa za su kasance masu ‘yan wasan baya da babu irinsu a gasara  wannan kaka.

Sai dai sa’o’i 48 da wannan duka da suka sha a hannu Liecester, City ta yunkuro ta dauko Ruben Diaz a kan fam miliyan 62, lamarin da ya kawo karshen matsalolinsu a fannin tsaron baya.

Tasirin Ruben

Dan wasan bayan na Portugal ya kawo karsashi da karfin tuwo a tawagar City, hakan ya bai wa John Stones kwarin gwiwa, suka yi aiki tare, suka kai ga gaci.

A wasani gasar Firimiya 10 da suka fara tare, kwallaye 2 ne kawai suka shiga ragar City, inda suka dauki maki 30.

Bayan taron gaggawa

Bayan da matsaloli suka yi wa Man City yawa, Kaftin din kungiyar Fernandinho ya kira wani taro don tattauna matsalolin da suka addabi kungiyar.

Tun bayan taron ne fa suka buga wasanni 21 ba tare da rashin nasara ba.

Sai da aka dage wasan City na karshe a kakar 2020 tsakaninsu da Everton sa’o’i gabanin fara shi saboda bullar annobar Coronavirus a tsakanin ‘yan wasansu.

Kasa da mako guda da wannan lamari City suka yi tattaki zuwa Stamford Bridge da manyan ‘yan wasansu 15 kawai saaboda sauran sun harbu daa coronavirus, kuma duk da haka suka samar da kwallaye 3 a mintuna 35.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.