Wasanni-Kwallon Kafa

Lokaci ya yi da zan bar Juventus - Buffon

Buffon ya sanar cewa zai bar Juventus.
Buffon ya sanar cewa zai bar Juventus. © AFP

Shahararren mai tsaron ragar Juventus, Gianluigi Buffon ya ce zai yi hannun riga da kungiyar da ke wasa a Serie A ta Italiya a karshen wannan kaka.

Talla

Buffon, mai shekaru 43, ya lashe kofunan Serie A har 10 da na kalubalen Italiya 4 a zamansa da Juventus sau biyu. Ya dawo Juventus daga PSG a 2019 bayan shafe kakanni 2.

Mai tsaron ragar ya shaida wa manema labarai cewa lokaci ya yi, saboda haka kamata ya yi ya bar kungiyar.

Buffon, wanda ya lashe kofin duniya da Italiya a shekarar 2006 ya kara da cewa dayan biyu ne, ko ya hakura da harkar murza tamaula kacokan, ko kuma idan ya samu inda ya ba shi sha’awa ya dan murza, yana mai cewa  a ganinsa ya yi duk abin da zai yi a Juventus, kuma ya samu duk abin da yake bukata a kungiyar.

Tsohon dan wasan tawagar Italiyar ya buga mata wasanni 176 a matakin kasa da kasa, kuma shine ya kafa tarihin dan wasan da ya fi kowanne taka leda a Serie A da wasanni 656.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.