Wasanni-Kwallon Kafa

Masu zakakuran 'yan wasa ne kawai za su iya kalubalantar Man City -Solskjaer

Manchester United manager Ole Gunnar Solskjaer
Manchester United manager Ole Gunnar Solskjaer Shaun Botterill POOL/AFP/File

Mai horar da ‘yan wasan Manchester United Ole Gunnar Solskjaer  ya yi kira ga masu kungiyar da su karfafa tawagarsa, bayan da rashin nasara 2-1  a gida a hannun Liecester City, a daren Talata ya tabbatar da Manchester City a matsayin wadanda suka lashe gasar Firmiya ta bana.

Talla

Wannan rashin nasara ya sa Man United su na bayan  Manchester City da maki 10, kuma maki 9 ne kawai suka rage wa United daga wasanni 3 da za su karkare gasar da su lamarin da ya sa aka mika wa City kofin.

Iyalan The Glazers, masu kungiyar Manchester  United sun sha suka da caccaka, da zanga zanga daga magoya bayan kungiyar a makonin da suka wuce biyo bayan yunkurinsu na shigar da kungiyar cikin gasar European Super League da ba ta yi farin jini ba.

Solskjaer ya ce idan har ana so a kalubalanci City, dole ne sai an sa kudi an sayi ‘yan wasa da za su karfafa tawagar.

Daga nan sai ya mika sakon taya murna ga Manchester City saboda wannan nasarar da suka samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.