Wasanni-Kwallon Kafa

Atletico Madrid na shirin lashe kofin La liga karo na 11 a tarihi

Wasu 'yan wasan Atletico Madrid.
Wasu 'yan wasan Atletico Madrid. JAVIER SORIANO AFP

Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, ta sake kama hanyar yiwuwar zama zakarar La liga a bana bayan shafe shekaru 7 ba tare da kai kofin gidanta ba, inda ta sake jan tazara tsakaninta da Kungiyoyin Real Madrid da Barcelona wadanda suka shafe shekaru suna lashe kofin.

Talla

Atletico bayan nasararta kan Real Sociedad a jiya, yawan tazarar da ke tsakaninta da Barcelona wadda ke gurbin ta biyu a teburin gasar ya zama maki 4, yayinda ita kuma Barcelonar ke da tazarar maki daya tal tsakaninta da Real Madrid kuma Madrid din na da kwantan wasa guda a hannu.

Atletico Madrid dai na tunkarar kofin na 11 ne a tarihi, kuma nasarar ta ta za ta tabbata ne idan har ta yi nasarar wasanninta biyu da suka rage.

Wasa na gaba da ke tunkaro kungiyar shi ne karawarta da Ossasuna a Lahadi 16 ga watan Mayun da muke sai kuma karawarta da Real Valladolid a ranar 18 ga wata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI