UEFA ta sauya filin wasan karshe na gasar zakarun Turai zuwa Portugal

Filin wasan da zai karbi wasan karshe na cin kofin zakarin Turai tsakanin Chelsea da Manchester City.
Filin wasan da zai karbi wasan karshe na cin kofin zakarin Turai tsakanin Chelsea da Manchester City. AP - Luis Vieira

Hukumar UEFA ta sanar da sauya filin da za a doka wasan karshe na cin kofin zakarun Turai, tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da Manchester City daga Ataturk Olympic Stadium na birnin Istanbul a Turkiya zuwa birnin Porto na Portugal.

Talla

Matakin sauya filin wasan ya biyo bayan tsanantar Covid-19 a Turkiya kasar da Tuni Birtaniya ta sanya ta a jerin masu fama da tsanantar cutar.

Kafin yanzu UEFA ta yi kokarin mayar da wasan filin Wembley amma dokokin yaki da Covid-19 ya ci karo da shirin hukumar na baiwa dubunnan magoya baya halartar wasan na karshe.

Sanarwar UEFA ta ce yanzu haka magoya bayan kungiyoyin biyu dubu 12 za su samu sukunin shiga kallon wasan na karshe a Portugal, wanda ke nuna kowacce kungiya za ta shiga wasan da magoya bayanta dubu 6 adadi mai yawa da za a gani a fili tun bayan bullar covid-19.

Shugaban hukumar ta UEFA Aleksander Ceferin ya ce sun mayar da wasan zuwa Porto ne bayan ganawarsu da mahukuntan Birtaniya a Larabar da ta gabata, inda suka ki amincewa da bukatar shigar ‘yan kallo filin wasan na Wembley.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI