Wasanni-Kwallon Kafa

Liverpool na bukatar nasara kan Crystal Palace don zuwa gasar zakarun Turai

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp. ANDREJ ISAKOVIC AFP/Archives

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce yanzu hankalinsu ya karkata ga wasansu da Crystal Palace ranar Lahadi wasan da zai tabbatar da gurbinsu a gasar cin kofin zakarun Turai.

Talla

A wasannin baya-bayan nan Liverpool ta bayar da mamaki ta yadda ta koma matsayin ta 4 a teburin daga ta 7 da ta ke a farkon watan nan, bayan nasararta kan West Brom a lahadin da ta gabata da kuma Burnley a jiya, ko da ya ke har yanzu akwai sauran rina a kaba, domin kuwa maki daya Liverpool din ta ke da Leicester wadda ke matsayin ta 5 in banda tazarar yawan kwallaye.

Yanzu haka dai wasa 1 ya ragewa dukkanin kungiyoyin na Firimiya 20 yayinda kungiyoyin Chelsea da Liverpool da kuma Leicester ke cikin tsaka mai wuya domin kuwa dole daya daga cikinsu ta rasa gurbin na ‘yan hudu, bayan da Manchester City ta dage kofin ita kuma Manchester United ta bai wa kungiyoyin 3 gagarumar.

Za a iya cewa kai tsaye Liverpool ka iya samun gurbi a gasar ta cin kofin zakarun Turai bayan tagwayen nasarorin sai dai Jurgen Klopp ya ce lokacin fara murna bai zo ba domin kuwa sai har sun yi nasara da tarin kwallaye a haduwarsu da Crystal Palace ne za su iya kere Leicester.

Wasan na ranar Lahadi dai zai zama na farko da Liverpool za ta buga tare da magoya bayanta a filinta na Anfield.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI