Wasanni

Arsenal ta rasa gurbi a wasannin Turai na badi karon farko cikin shekaru 25

'Yan wasan Arsenal yayin wasan su da Fulham
'Yan wasan Arsenal yayin wasan su da Fulham FACUNDO ARRIZABALAGA POOL/AFP

Arsenal ta kafa mummunar tarihin wajen rasa gurbin samun damar zuwa wasan kwallon kafa na Turai karon farko cikin shekaru 25.

Talla

Sakamakon yadda ta gaza zama cikin na 1 zuwa har na 7 a saman teburin gasar ta Ingila, inda ta karkare a ta 8 da maki 61.

Tottenham ta yi duk mai yiwuwa wajen samun gurbi  a gasar Europa League bayan doke Leicester city da 3 -2 a ranar karshe ta kakar.

Hakan na nufin Arsenal ba za ta buga wasan kwallon kafa a Turai ba a kakar wasa mai zuwa a karon farko tun kakar shekarar 1995-96.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI