Wasanni - kwallon kafa

Kungiyoyin da suka lashe gasar wasannin Lig-Lig na Turai

Yadda Atlético Madrid da magoya bayan ta suka chashe nasarar lashe gasar Lilagar Spain ranar 22 ga watan Mayu 2021.
Yadda Atlético Madrid da magoya bayan ta suka chashe nasarar lashe gasar Lilagar Spain ranar 22 ga watan Mayu 2021. Óscar del Pozo AFP

Atletco Madrid ta yi nasarar daukar kofin La Liga na bana, bayan da ta doke Real Valladolid da ci 2-1 a wasan mako na 38 na karshe a kakar 2020/21 a Spaniya.

Talla

Luis Suarez ya kasance cikin hawaye ranar Asabar bayan kwallon da ya ci ya taimakawa Atletico Madrid daukar kofin La Ligar, yana mai godiya ga kungiyar da ta cece shi.

Dan kasar Uruguay din, wanda ya koma Madrid daga Barcelona a watan Agusta, ya gode wa "Atletico saboda bude musu kofofinsu."

Dan wasan Atletico Madrid Luiz Suarez da abokan taka ledarsa yayin wasan karshe na Liliga 22 ga watan Mayu 2021.
Dan wasan Atletico Madrid Luiz Suarez da abokan taka ledarsa yayin wasan karshe na Liliga 22 ga watan Mayu 2021. REUTERS - JUAN MEDINA

Madrid da Barcelona da Sevilla sukayi na 2 da na uku na hudu, kuma suka samu tikitin gasar Zakarun Turai mai zuwa.

EPL - Ingila

A gasar Premier Ingila kuwa, Manchester City ce ta lashe kofin na bana, bayan da Manchester United ta yi rashin nasara 2-1 a hannun Leicester City a Old Trafford.

City ce ta yi ta daya a bana sai United ta biyu a teburi, sannan Liverpool ta uku da Chelsea ta hudun da za su wakilci Ingila a Champions League a kakar badi.

Manchester City yayin murnar lashe gasar Premier League 23 ga watan Mayun 2021.
Manchester City yayin murnar lashe gasar Premier League 23 ga watan Mayun 2021. PETER POWELL POOL/AFP

Seria A – Italiya

Inter Milan tayi bukin Lashe kofin Seria A na bana gaban magoya banya na cikin gida, bayan doke Udinese da ci biyar da 1 a wasan karshe da aka fafata jiya Lahadi.

Inter ce tayi na daya a bana, sai Milan ta biyu a teburi, sannan Atalanta ta uku sai kuma Jeventus da ta sha dakyar wajen samun tikitin zuwa Champions League mai zuwa.

Magoyaban Inter Milan dake murnar nasarar lashe gasar Seria
Magoyaban Inter Milan dake murnar nasarar lashe gasar Seria REUTERS - FLAVIO LO SCALZO

Bundesliga – Jamus

Bayern Munich ce ta lashe kofin, a matsayin ta daya a saman teburi, sai Leipzig ta biyu sannan Dortmund ta uku sai kuma Wolfsburg ta hudu a wadanda zasu wikilci kasar a zakarun Turai ta badi.

'Yan wasan Bayern Munich yayin nasarar lashe gasar Bundesliga karo na 6 a jere.
'Yan wasan Bayern Munich yayin nasarar lashe gasar Bundesliga karo na 6 a jere. Pool via REUTERS - MATTHIAS SCHRADER

Ligue 1 - Faransa

A gasar Ligue 1 na kasar Faransa kuwa Lille ta sha gaban PSG ta lashe kofin na bana, yayin da PSG da Monaco da Lyon suka samu tikitin wakiltar kasar a gasar zakarun Turai ta badi, amatsayin na daya zuwa na hudu.

'Yan wasan Lille da sukayi nasarar lashe gasar Ligue 1 na Faransa
'Yan wasan Lille da sukayi nasarar lashe gasar Ligue 1 na Faransa © AP - Lewis Joly

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.