Wasanni

Ronaldo ya kafa tarihin zama dan wasan da ya fi cin kwallo a manyan gasanni

Dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo
Dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo ALBERTO LINGRIA POOL/AFP

Cristiano Ronaldo ya kara kafa tarihi a ranar Lahadi, inda ya zama dan wasa na farko da ya kammala kakar a matsayin dan wasan da ya fi kowa cin kwallaye a manyan Lig-Lig uku – wato Ingila da Spain da kuma Italiya.

Talla

Ronaldo mai shekaru 36 ya ci kwallaye 29 a wannan kaka, wanda ya dara na Romelu Lukaku  a Inter Milan.

Dan wasan na Portugal ya kasance dan wasan da ya fi zura kwallaye a Ingila tare da Manchester United a 2008, kuma sau uku a Spain tare da Real Madird, a shekarar 2011 da 2014 da kuma 2015.

Amma wannan shine karo na farko cikin kaka uku da dan wasan da ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar ya fi cin kwallaye, inda ya samu jummular kwallaye 101 a Juventus.

A ranar Lahadi, ya kasance a kan benci a wasan karshe na Juventus a wasan da suka doke Bologna da ci 4-1 wanda hakan ya ba kungiyar damar kammala gasar cikin hudun farko da zasu shiga gasar neman cin kofin zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI