Wasanni-Kwallon Kafa

Conte ya raba gari da Inter Milan bayan ya taimake ta

Antonio Conte
Antonio Conte Lars Baron POOL/AFP/File

Manajan Kungiyar Inter Milan tar Italiya Antonio Conte ya ajiye aikinsa kwanaki bayan ya jagoranci kungiyar har ta lashe gasar Serie A a karon farko cikin shekaru 11.

Talla

Kungiyar Inter Milan ta ce,  sun cimma matsaya da Conte ta raba gari cikin mutunci, saboda haka babu wata baraka a tsakaninsu.

Sanarwar kungiyar ta gode wa manajan saboda rawar da ya taka wajen daga darajarta ta hanyar lashe gasar Serie A wanda shi ne karo na 19 da kungiyar ta yi nasarar lashewa.

Conte da ya jagoranci kungiyoyi irin su Chelsea da Juventus ya karbi ragamar aikin horas da Inter Milan ne a watan Mayun shekarar 2019 akan Dala miliyan 14.

Rahotanni sun ce, an samu takun-saka tsakanin Conte da kungiyar saboda rashin kudin sayen kwararrun 'yan wasa, abin da ya hana shi dauko manyan 'yan wasan Turai.

A shekarar da ta gabata, kungiyar Inter Milan ta sanar da asarar Euro miliyan 100 sakamakon illar da annobar korona ta yi wa kungiyoyin kwallon kafa saboda rashin 'yan kallo.

Rahotanni sun ce, ana saran Conte ya karbi aikin ragamar horas da Real Madrid ko Tottenham Hotspur.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI