Wasanni - Kasuwanci

Kamfanin Nike ya soke yarjejeniyar dake tsakaninsa da Neymar

Fitaccen dan wasan Brazile dake kungiyar PSG Neymar, yayin fita daga babban ofishin 'yan sanda a birnin Rio de Janeiro cikin watan Yunin 2019.
Fitaccen dan wasan Brazile dake kungiyar PSG Neymar, yayin fita daga babban ofishin 'yan sanda a birnin Rio de Janeiro cikin watan Yunin 2019. © REUTERS/Lucas Landau

Kamfanin samar da sutura da takalma na Nike, ya sanar da soke kwangilar tallata kayayyakin nasa da ya kulla da Neymar, fitaccen dan wasan Brazil dake taka leda a kungiyar PSG.

Talla

Nike ya ce ya dauki matakin ne sakamakon kin bayar da hadin kan da Neymar yayi ga masu binciken zargin da wata ma’aikaciyarsu ke yiwa dan wasan na neman cin zarafinta ta hanyar lalata da ita.

Lamarin dai ya auku ne a shekarar 2016, to amma sai a shekarar 2018, ma’aikaciyar ta gabatar da korafin cin zarafin nata da Neymar yayi.

Dan wasan dai na cigaba da musanta aikata laifin, tare da caccakar kamfanin na Nike dangane da katse alakar kasuwancin dake tsakaninsu ba tare da gabatar da hujjojin zartas da hukunci kan zargin da ake masa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI