Wasanni-Kwallon Kafa

Firimiya ta fitar da jerin 'yan wasan da za ta zabi gwarzon bana a ciki

Manchester City bayan dage kofin Firimiya na 3 cikin shekaru 4.
Manchester City bayan dage kofin Firimiya na 3 cikin shekaru 4. PETER POWELL POOL/AFP

‘Yan wasan Manchester City Kevin de Bruyne da Ruben Dias sun shiga sahun jerin ‘yan wasan da za a zabi zakaran Firimiya na bana a cikinsu, gasar da a wannan karon kungiyarsu ta sake lashewa karo na 3 a cikin shekaru 4.

Talla

Sauran ‘yan wasan da ke cikin jerin sun hada da Harry Kane na Tottenham wanda ya lashe kyautar Golden Boot ko kuma takalmin zinare na bana bayan kasancewa mafi zura kwallaye karkashin wasannin gasar ta firimiya, kana Mohammed Salah na Liverpool da kuma Bruno Fernandes na Manchester United.

Haka zalika akwai Mason Mount na Chelsea da Tomas Soucek na West Ham United da kuma Jack Grealish na Aston Villa.

A bangaren Masu horarwa akwai Pep Guardiola na Manchester City akan gaba kana takwaransa na Leeds United Marcelo Bielsa da David Moyes na West Ham kana Brendan Rodgers na Leicester City da kuma Ole Gunnar Solskjear na Manchester United.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.