Wasanni-Brazil

Bolsonaro ya kare matakin Brazil na karbar bakoncin gasar Copa America

Tawagar Brazil a filin wasa na Maracana bayan dage kofin Copa America a 2019.
Tawagar Brazil a filin wasa na Maracana bayan dage kofin Copa America a 2019. Carl DE SOUZA AFP/File

Shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro yak are matakin kasar na shirin karbar bakoncin gasar COPA America da Argentina ta sanar da janyewa daga daukar nauyinta biyo bayan tsanantar coronavirus.

Talla

Bolsonaro wanda ya bayyana shirin daukar nauyin gasar a matsayin babbar dama ga Brazil ya gamu da kakkausar suka daga sassan kasar la’akari da yadda cutar zuwa yanzu ke ci gaba da tsananta bayan kisan mutane dubu 463.

A cewar Bolsonaro ya zanta da ministan Lafiya na kasar da sauran masana kiwon lafiya dangane da ko karbar bakoncin gasar zai yiwa kasar illa, tun gabanin ya yi maraba da matakin, wanda y ace bisa shawarwarinsu ne yayi maraba da matakin.

Shugaban na Brazil wanda ya bayyana kofin na COPA America a matsayin wanda kasar ke hari a yanzu ya bukaci ‘yan wasan kasar da su jajirce wajen dageshi a wannan karon.

Gasar ta Copa America wadda za ta fara a makon gobe, za ta gudana a kasar ta Brazil ne bayan da Artgentina ta janye a bangare guda kuma hukumar da ke kula da ita ta ki amincewa da mikata ga Venezuela.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.