Wasanni-Kwallon Kafa

Carlo Ancelotti ya karbi ragamar horar da Real Madrid a karo na 2

Carlo Ancelotti tare da shugaban Real Madrid Florentino Pérez.
Carlo Ancelotti tare da shugaban Real Madrid Florentino Pérez. DOMINIQUE FAGET AFP/Archivos

Sabon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Carlo Ancelotti ya bar Everton yau Laraba don karbar ragamar horar da tsohuwar kungiyar sa da ya ke shirin rattaba hannu kan kwantiragin shekaru 3 tsakaninsa da ita kowanne lokaci daga yanzu.

Talla

Ancelotti dan Italiya mai shekaru 61 wanda ya taba horar da Real Madrid tsakanin 2013 zuwa 2015 tare da dagewa kungiyar kofin zakarun Turai, sabuwar yarjejeniyar tsakaninsa da tsohuwar kungiyar tasa na nuna cewa watanni 18 kacal ya yiwa Everton duk da cewa yarjejeniyar shekaru 4 ke tsakaninsa da ita.

Karbar aikin horar da Real Madrid din don maye gurbin Zinadine Zidane da Ancelotti ya yi, ya bar Everton da laluben manaja na din din din karo na 6 a shekaru 5.

Yau Laraba ne Ancelotti zai bayyana a taron manema labarai na Real Madrid don tsokaci kan muradan da ya ke kokarin cimmawa a kungiyar bayan da ya bayyana matakin sake daukarshi aikin a matsayin mai cike da bazata.

A cewar Ancelotti duk da yanajin dadin aiki a Everton amma komawa Spain zai fi masa kwanciyar hankali har ma da iyalinsa baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI