Wasanni-Kwallon Kafa

Ancelotti ya kawo karshen shakku kan makomar Hazard da Bale a Madrid

Eden Hazard yayin karawar Real Madrid da PSG a watan Nuwamban 2019 a gasar zakarun Turai.
Eden Hazard yayin karawar Real Madrid da PSG a watan Nuwamban 2019 a gasar zakarun Turai. AFP/Archives

Sabon mai horas da Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce yana bukatar kasancewar Eden Hazard da kuma Gareth Bale cikin tawagarsa a sabuwar kakar wasa.

Talla

Matsayarsa da Ancelotti da ya bayyana yayin taron manema labarai na farko da yayi a jiya Laraba bayan sake karbar ragamar horas da Real Madrid ya kawo karshen cece-kucen da ake y ikan makomar Hazard da Bale da ake zaton nan bada dadewa ba za su rabu da kungiyar.

Tun bayan komawa Madrid daga Chelsea a a watan Yulin 2019, Hazard ya kasa taka irin rawar da yayi a tsohuwar kungiyarsa sakamakon fama da raunukan da suka janyo masa rasa buga wasanni akalla 41.

Gareth Bale
Gareth Bale Richard Heathcote POOL/AFP

Shi kuwa Gareth Bale da dagantaka tayi tsami tsakaninsa da tsohon Kocin Real Madrid Zinaden Zidane, ya kasance tare da kungiyar Tottenham ne a matsayin aro, a tsawon kakar wasan da ta kare, inda ya ci kwallaye 14 duk da cewar bai buga adadin wasanni da yawa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.