Wasanni-Kwallon Kafa

Babu dan wasan tsakiya kamar Kante a nahiyar Turai - Wenger

Chelsea's French midfielder N'Golo Kante
Chelsea's French midfielder N'Golo Kante Matt Dunham POOL/AFP/File

Tsohon mai horas da kungiyar Arsenal Arsene Wenger ya bayyana tauraron Chelsea N’Golo Kante a matsayin dan wasan tsakiyar da babu kamarsa a nahiyar Turai.

Talla

Wenger ya kare zabin nasa da hujjar cewar, baya ga iya rabawa abokan wasansa kwallo dalla dalla, Kante yayi matukar kwarewa wajen karbe kwallon daga abokan hamayyarsa ba tare da yin keta ba, yayin da kuma zai yi wahala ka gay a janyowa tawagarsa asarar kwallo daga kafarsa, abinda ya bashi damar karawa Chelsea karfin kaiwa abokan karawarta hare-haren neman cin kwallo.

Dan wasan tsakiya na kungiyar Chelsea N'Golo Kante
Dan wasan tsakiya na kungiyar Chelsea N'Golo Kante AFP

Kante mai shekaru 30 ya samu wanan matsayi tsakanin masana tamaula ne tare da kuma na cigaba samun yabo, bayan da ya zama gwarzon dan wasa yayin wasannin gida da waje da suka kara da Real Madrid a zagayen kusa da na karshen gasar cin kofin Zakarun Turai, da kuma wasan karshen da suka samu nasara kan Manchester City da 1-0.

Kwazo da kwarewar da Kante ya nuna ta sanya shi zama cikin jerin ‘yan wasan da ake ganin za su iya lashe gagarumar kyautar gwarzon dan wasan duniya ta Ballon d’Or da kuma hukumar FIFA.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.