Wasanni - Tennis

Serena na gaf da isa zagayen siri daya kwale a gasar French Open

Fitacciyar 'yar wasan kwallon Tennis a duniya Serena Williams bayan samun nasarar kaiwa zagayen gasar French Open na 3.
Fitacciyar 'yar wasan kwallon Tennis a duniya Serena Williams bayan samun nasarar kaiwa zagayen gasar French Open na 3. © Pierre Rene-Worms/RFI

Fitacciyar 'yar kwallon Tennis a duniya Serena Williams 'yar Amurka, ta samu nasarar tsallakawa zagaye na uku na babbar gasar Grand Slam ta French Open ajin mata da kuma maza dake gudana a Faransa.

Talla

Serena mai shekaru 39 ta samu nasarar ce bayan doke Mihaela Buzrnescu ta kasar Romania da 6-3, 6-1, yayin da tayi rashin nasara sau daya da 5-7, a zagaye ukun da suka fafata.

Serena Williams na neman lashe kofin gasar ta French Open ne karo na 4, wanda kuma shi ne na farko tun bayan wanda ta dauka a shekarar 2015.

Mai yiwuwa dai a wannan karon burin fitacciyar ‘yar wasan ya cika a bana, la’akari da cewar Simona Halep da ta doke ta a wasan karshe na gasar kwallon tennis din ta Grand Slam amma ta Wimbledon a 2019, ta janye daga shiga gasar ta French Open saboda rashin lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.