Guardiola ba ya kaunar mu - Mahaifin Aguero
Wallafawa ranar:
Mahaifin Sergio Aguero ya bayyana cewa lallai Arsenal da Chelsea sun nemi dansa ya taka musu leda, kana ya caccaki Pep Guardiola kan yadda ya wulakanta tsohon dan wasan gaban na Machester City.
Dan wasan gaban mai shekaru 33 ya bar kungiyar Manchester City ne a matsayin dan wasan da ya fi kowanne jefa kwallo a tarihin kungiyar, inda ya koma a Barcelona a ba tare da City ta ci wani rib aba.
Ya samu damammakin komawa kungiyoyi da dama a Ingila amma ya zabi ya hade da dan kasarsa, wato kaftin din Argentina, Lionel Messi a Camp Nou.
Leonel Del Castillo ya shaida wa wata tashar rediyo a sha’awar Aguero ta komawa Barcelona, yana mai cewa dansa yana farin cikin matakin da ya dauka.
Da aka tambaye shi ko yaya ya ga hawayen da Guardiola ya zubar a lokacin da ya ke magana a kan tafiyar Aguero, sai ya ce duk bulla ce, saboda baya kaunarsa da iyalansa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu