Na ji dadin sake dawowar Ancelotti a matsayin kocin Madrid- Hazard
Wallafawa ranar:
Eden Hazard ya bayyana farin cikinsa a game da nadin Carlo Ancelotti a matsayin sabon kocin kungiyar Real Madrid, yana mai cewa hakan yana da matukar kyau a gare ni.
Ancelotti ya koma Real Madrid ne bayan da ya yi hannun riga da Everton a karo na biyu a ranar Talata, inda ya sanya hannu a kwantiragin zaman shekaru 3 a Santiago Bernabeu.
Hazard yana sa ran aiki da dan kasar Italiyan, wanda ya maye gurbin Zinedine Zidane, kuma yana jin cewa Real Madrid za ta ba mara da kunya a karkashin jagorancinsa.
Ancelotti ne ya gaji Jose Mourinho a Santiago Bernabeu a shekarar 2013, inda daga nan ne ya lashe kofuna 3 da tawagar a cikin kakar wasa 2, ciki har da kofin Copa del Rey da na FIFA World Club na zakarun kungiyoyin duniya.
Jigo a cikin jerin gudummawar da Ancelotti ya bayar a Madrid shine lashe kofin zakarun Turai na 10, wato La Decima, inda Madrid ta doke Atletico Madrid a wasan karshe a shekarar 2013-14 don cin kofin a karo na 10.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu