Wasanni

CAF ta jinkirta lokacin fitar da jadawalin gasar kofin Afirka

Kofin gasar kwallon kadar Afrika CAF
Kofin gasar kwallon kadar Afrika CAF AFP

Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka CAF ta sanar da dage bukin fitar da jadawalin gasar cin kofin Afirka da ke tafe a shekarar 2022 a kasar Kamaru.

Talla

CAF ta bayyana tasirin cutar kwaronavirus a matsayin dalilin dage zama shirya jadawalin, wanda ya kamata ayi shi, a Yaounde babban birnin kasar Kamaru ranar 25 ga watan Yuni, ba tare da sanya wata sabuwar rana ba.

Tun cikin shekarar 2020 ya kamata a buga wasannin gasar na neman cin kofin Afirka da Kamaru zata karbi bakwanci amma aka dage saboda barkewar annobar korona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.