Wasanni-Kwallon Kafa

Real Madrid da Manchester United na cikin masu zawarcin Ronaldo

Dan wasan Juventus, Cristiano Ronaldo.
Dan wasan Juventus, Cristiano Ronaldo. Isabella BONOTTO AFP

Cristiano Ronaldo yana nazari a kan kungiyoyin da suke bukatar ya murza musu tamaula a kaka mai zuwa biyo bayan jita-jitar cewa akwai yiwuwar zai bar Juventus a wannan bazarar.

Talla

Wakillan dan wasan mai shekaru 36 su na duba bukatun da kungiyoyi da dama suka mika na dan wasan, kuma cikin kungiyoyin da ke neman sa har da Paris St Germain da tsaffin kungiyoyinsa Real Madrid da Manchester United.

Masu tafiyar da harkokin na Ronaldo ba za su yanke shawara a game da makomar dan wasan ba har sai bayan gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2020, amma sun ce lallai akwai yiwuwar canza sheka za ta yi wuya, saboda albashin da za a rika biyansa da kuma farashin da Juventus ta sanya a kansa sun yi yawa.

Ronaldo ya riga ya tattauna da sabon kocin Juventus Massimiliano Allegri bayan da ya maye gurbin Andrea Pirlo  a matsayin mai horas da kungiyar da ke Turin na kasar Italia, kuma an shirya karin tattaunawa kafin kungiyar Serie A din ta fara atisayen tarbar kaka mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.