Wasanni-Kwallon Kafa

Tottenham ta sanya farashin Fam miliyan 150 a kan Kane

 Harry Kane, dan wasan Tottaenham.
Harry Kane, dan wasan Tottaenham. PAUL CHILDS POOL/AFP/File

Tottenham za ta bukaci zunzurutun kudi har Fam miliyan 150 a kan dan wasanta Harry Kane, a cinkin tsabar kudi kawai, ba tare da an hada mata da wani dan wasa ba, kamar yadda jaridar The Sun ta ruwaito.

Talla

Wannan ka’ida na zuwa ne a yayin da Manchester City ta bayyana aniyar mika wa Tottenham manyan ‘yan wasanta biyu, Raheem Sterling da Gabriel Jesus don kai ga gaci a cinikin.

Kane na daya daga cikin ‘yan wasan da aka fi nema  da ke kasuwa a halin yanzu, bayan da ya saka kwallaye 23, ya kuma taimaka aka ci 14 a kakar da aka karkare kwanan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.