Wasanni - Kwallon Kafa

Firimiya ta ci tarar kungiyoyi 6 saboda gasar Super League

Wata sanarwar nuna adawa da kirkirar sabuwar gasar Super League a kofar shiga filin Anfielde na kungiyar Liverpool.
Wata sanarwar nuna adawa da kirkirar sabuwar gasar Super League a kofar shiga filin Anfielde na kungiyar Liverpool. Paul ELLIS AFP

Hukumar gudanarwar gasar Firimiyar Ingila ta ce kungiyoyin nan shida dake karkashinta da suka hada da Arsenal, Manchester United, Manchester City, Tottenham, Chelsea da kuma Liverpool za su biya tarar fam miliyan 22, sakamakon laifin da suka aikata na hada kai domin shirya kafa sabuwar  gasar Super League a nahiyar Turai.

Talla

Hukumar Firimiyar ta kuma ce dukkanin kungiyoyin sun amince da fuskantar hukuncin tilasta musu biyan tarar fam miliyan 25 da kuma ragewa kowaccensu maki 30-30, muddin suka sake aikata makamancin laifin na kokarin ballewa ko kafa wata sabuwar gasa a nan gaba.

A farkon watan Mayun da ya gabata hukumar kula da kwallon kafar nahiyar Turai UEFA ta bayyana soma nazari kan daukar matakin hukunta kungiyoyin kwallon kafar da suka yi yunkurin kafa sabuwar gasar Super League, wadanda kuma har yanzu suka ki janye aniyar tasu duk da cikas din da ta gamu da shi.

Muddin hukumar ta UEFA ta cimma matsayar ladabtar da wadannan kungiyoyi, hukuncin ka iya zama haramta musu buga wasannin gasar cin kofin zakarun turai ko na Europa har na tsawon shekaru 2.

A waccan lokacin UEFA ta bayyana samun nasarar  tattaunawa da kungiyoyi 8 daga 12 da suka yi yunkurin kafa sabuwar gasar ta Super League, kan yiwuwar sassauta musu hukunci.

Ragowar kungiyoyi 4 da suka rage, Juventus, Barcelona, AC Milan da kuma Real Madrid kuwa na kan aniyar kafa sabuwar gasar, domin a cewar su takardun da suka gabatarwa hukumar FIFA da UEFA sun nuna neman izinin gudanar sabuwar gasar ce, ba wai son ballewa daga gasar cin kofin zakarun Turai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI