Wasanni-Tennis

Novak Djokovic ya kai wasan gab da na karshe a gasar French Open

Djokovic bayan nasarar tsallakawa wasan gab da na karshe na French Open.
Djokovic bayan nasarar tsallakawa wasan gab da na karshe na French Open. © Pierre René-Worms/ RFI

Novak Djokovic ya yi nasarar doke takwaransa na Italiya Matteo Berrettini a wasansu na gab da na kusa da karshe karkashin gasar French Open, wasan da ya gudana a gaban ‘yan kallo dubu 5 a birnin Paris, ko da ya ke dokar hana yawon dare da ke farawa daga karfe 11 na dare ta tilastawa ‘yan kallo ficewa daga fili gabanin karkare wasan.

Talla

Nasarar ta Djokovic dan Serbia da kwallaye 6-3 6-2 da 6-7 sannan 7-5 sun bashi damar tsallakawa wasan gab da na karshe inda zai kara da Rafael Nadal, haduwar da za ta zama irinta ta 58 da zakarun na Tennis suka yi a tarihi.

Kafin karkare wasan dai wanda ya ja lokaci, ‘yan kallo sun rika sowar bukatar tsayar da shi saboda dokar hana yawon dare.

Haduwar ta Djokovic da Nadal za ta sabunta dabin da ke tsakaninsu tsawon shekaru dai dai lokacin da dan wasan na Serbia mai shekaru 34 ke kokarin kara yawan kambunsa a Roland Garros zuwa 14.

Djokovic, dai ya dara takwarorinsa Nadal da Federer bayan lashe Grand Slam karo na 18 yayin gasar Australian Open a watan Fabarairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.