Wasanni-Kwallon Kafa

Ronaldo da Fernandes sun kai Portugal ga nasara kan Isra'ila

Cristiano Ronaldo bayan tashi daga wasansu da Isra'ila.
Cristiano Ronaldo bayan tashi daga wasansu da Isra'ila. REUTERS - SERGIO PEREZ

Cristiano Ronaldo na Juventus da Bruno Fernandes na Manchester United sun zura kwallayen da suka baiwa Portugal nasarar lallasa Isra’ila a wasan sada zumuncin da suka doka a daren jiya Laraba.

Talla

An dai ta shi wasa Portugal na da 4 Isra’ila na nema, wasannin da ke zuwa gabanin bude gasar cin kofin kasashen Turai ta EURO 2020 a gobe juma’a 11 ga wata.

Farnandes ya fara zurawa Portugal kwallonta na farko a minti na 42 da fara bisa taimakon Joao Cancelo gabanin Ronaldo ya zura kwallo ta biyu a tazarar minti biyu cal da kwallon farnandes.

Sai bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne Cancelo ya zurawa Portugal kwallonta na 3 a minti na 86 da fara wasa yayinda Farnandes ya zura ta 4 a minti na 91 gab da karkare wasa.

Sai a ranar Talata mai zuwa ne Portugal za ta doka wasanta na farko karkashin gasar ta euro bayan budeta a gobe, wadda za a shafe wata guda ana wasanninta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.