Wasanni-Kwallon Kafa

Tottenham na zawarcin Fonseca na Roma don maye gurbin Mourinho

Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta AS Roma Paulo Fonseca.
Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta AS Roma Paulo Fonseca. Tiziana FABI AFP

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta fara tattaunawa da tsohon kocin AS Roma Paulo Fonseca a wani yunkuri na kulla kwantiragi da shi da nufin jan ragamar kungiyar bayan korar Jose Mourinho a kakar da ta gabata.

Talla

Tattaunawa da Fonseca ta biyo bayan tabarbarewar makamanciyarta da Antonio Conte wanda a farko Tottenham ta so kulla kwantiragi da shi amma kuma bangarorin biyu suka gaza cimma jituwa kan daukar horarwa.

A bangare guda, Fonseca ya rasa aikinsa da Roma ne duk da bajintar da ya nuna a wannan kaka, amma kuma kungiyar ta gaza kai labari tare da karkare Serie A a matsayin ta 7, yayinda Manchester United ta yi waje da ita a gasar Europa.

Cikin watan Aprilu ne Tottenham ta raba gari da Jose Mourinho bayan jerin rashin nasarori a wasanninsu na Firimiya da Europa, sai dai duk da korar ta sa Tottenham ta ci gaba da fuskantar matsaloli, yayinda ta rasa wasan karshe na Europa.

Kungiyar ta Tottenham wadda ta kammala Firimiyar bana a matsayin ta 7 a teburi, kai tsaye ta rasa gurbi a gasar cin kofinn zakarun Turai yayinda ta ke bukatar sabon mai horarwa don murmurowa a kaka mai zuwa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI