Wasanni - Kwallon Kafa

PSG ta kulla yarjejeniyar shekaru 3 da Wijnaldum

Georginio Wijnaldum
Georginio Wijnaldum © Reuters/Jason Cairnduff

PSG ta kulla yarjejeniyar shekaru uku da dan wasan Liverpool Georginio Wijnaldum mai shekaru 30.

Talla

Wijnaldum zai raba gari da Liverpool ne a matsayin dan wasa mai zaman kansa sakamakon karewar da yarjejeniyar za ta yi da kungiyar a karshen wannan wata.

A dai kungiyar Barcelona aka sa ran za ta kulla yarjejeniya da tsohon dan wasan, amma aka samu sauyin da ya sanya shi amincewa da tayin kungiyar PSG.

Kafin rabuwa da Liverpool, Wijanaldum ya s hafe shekaru 5 tare da ita, inda ya taka muhimmiyar rawa a kakar wasa ta 2019 da suka lashe kofin gasar zakarun Turai, da kuma gasar Firimiyar Ingila a shekarar bara ta 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.