Wasanni - Kwallon Kafa

Ukraine za ta soke kalaman siyasar dake rigar tawagar 'yan wasanta

Rigar 'yan wasan kwallon kafa na tawagar kasar Ukraine.
Rigar 'yan wasan kwallon kafa na tawagar kasar Ukraine. © EPA / TASS

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai UEFA ta baiwa Ukraine umarnin cire alamar siyasar da ke jikin rigar tawagar ‘yan kwallon kafar kasar dake cikin gasar cin kofin kasashen nahiyar Turan da za a soma a yau.

Talla

“Glory to the Heroes” abinda ke nufin “jinjina ga jarumai” shi ne abinda ke rubuce a rigar ‘yan wasan na Ukraine, kalaman da aka rika amfani da su yayin zanga-zangar adawa da gwamnatin Rasha a kasar ta Ukraine cikin shekarar 2014, matakin da UEFA tace ya saba doka, la’akari da alakarsa da siyasa.

Bayanai sun ce a baya dai hukumar UEFA ba ta nemi soke wadannan kalamai ba, sai bayan da Rasha ta aike mata da wasikar korafi kan kalaman siyasar dake rubuce a rigunan tawagar kwallon kafar na Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.