Wasanni - Kwallon Kafa

Salah ya sake lashe kyautar gwarzon gasar Firimiya

Mohammed Salah
Mohammed Salah REUTERS/Andrew Yates

Tauraron kungiyar Liverpool Mohammed Salah ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na gasar Firimiyar Ingila da aka kammala a kakar wasa ta 2020/2021.

Talla

Karo na biyu kenan da dan wasan ke lashe wannan kyauta, da kuma ta talamin Zinare tun bayan kulla yarjejeniya da Liverpool a shekarar 2017.

Salah ya ciwa kungiyar tasa kwallaye 31 da kuma taimakawa wajen cin wasu 6 a dukkanin wasanni 50 da ya haskawa Liverpool. Yayin da a gasar Firimiya ya ci kwallaye 22 jumilla tare da taimakawa wajen jefa wasu 5.

Kungiyar ta Liverpool dai ta karkare kakar wasan da aka kammala ne a matsayi na 3 bayan Manchester United da kuma Manchester City da ta lashe kofin gasar Firimiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI