Wasanni - La Liga

Sevilla ta yiwa Ramos tayin yarjejeniya mai romo

Sergio Ramos.
Sergio Ramos. AFP/Archives

Bayanai daga majiyoyi kwarara a Spain sun ce kungiyar Sevilla ta ce a shirye take ta sake kulla yarjejeniyar shekaru 5 da kaftin din kungiyar Real Madrid Sergio Ramos.

Talla

Ramos mai shekaru 35 ya taka leda a kungiyar Sevilla ne a ajin matasa kafin sauya sheka zuwa Real Madrid a shekarar 2005, inda kawo yanzu ya shafe shekaru 16 yana haskawa.

Tun a farkon kakar wasan da aka karkare ne dai ake ta cece-kuce kan makomar Sergio Ramos a Real Madrid wanda yarjejeniyarsa da kungiyar ke shirin karewa a karshen wannan wata na Yuni, la’akari da cewa a watanni baya dan wasan ya ki amincewa da tayin sabuwar yarjejeniyar da aka mika masa.

Baya ga kungiyar Sevilla dai, an dade ana alakanta kaftin din na Madrid da komawa kungiyoyin PSG ko kuma Manchester United.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI