Damben Boxing

Zan kawo Damben Boxing na UFC zuwa Afirka - Kamaru Usman

Zakaran damben boxin ajin Welter na UFC Kamaru Usman dan asalin Najeriya
Zakaran damben boxin ajin Welter na UFC Kamaru Usman dan asalin Najeriya Stephen R. Sylvanie/Reuters

Shahareren dan damben Boxin na duniya ajin mai biye da na tsaka-tsakar nauyi, Kamaru Usman mai rike da kambun ajinsa na UFC, na ziyara a Najeriya kasar sa ta asili karon farko cikin shekarin 26, inda yace zai kawo wasan nahiyar Afirka masamman Najeriya.

Talla

Usman, wanda  ba a doke shi ba a wasanni 18, gami da nasarori 14 a jere, ya gana da manema labarai a birnin Legas yau Lahadi, inda ya bayyana musu cewa, ako da yaushe gabanin soma fafatawa sai ya ji fargaba cikin zuciyarsa, amma kuma sai ya samu nasara.

Zakaran damben boxin ajin Welter na UFC Kamaru Usman.
Zakaran damben boxin ajin Welter na UFC Kamaru Usman. Getty Images via AFP - ALEX MENENDEZ

Matashin mai shekaru 33, wanda shine dan Afirka na farko a tarihin UFC, ya ce yana shirin kawo wasannin UFC zuwa Afirka, bayan da Nahiyar ta samar da irinsa guda uku a zakarun gasar.

Zakaran damben boxin ajin Welter na UFC Kamaru Usman.
Zakaran damben boxin ajin Welter na UFC Kamaru Usman. Chris Unger/Zuffa LLC/Zuffa LLC via Getty Images

Yayin da Usman ya kasance zakara a rukunin masu biye da tsakatsakan nauyi, Israel Adesanya shima dan Najeriya shi ne zakaran matsakaita nauyi sai kuma Francis Ngannou na Kamaru wanda ke zakaran ajin masu nauyi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.