EURO 2020

Faransa ta samu maki uku dakyar a hannun Jamus da ci 1 - 0

'Yan wasan Faransa da Jamus yayin fafatawa a gasar Euro 2020, ranar 15 ga watan Yuni 2021
'Yan wasan Faransa da Jamus yayin fafatawa a gasar Euro 2020, ranar 15 ga watan Yuni 2021 Matthias Schrader POOL/AFP

Faransa dake rike da kambin kofin duniya ta fara wasannin gasar Euro 2020 da kafar dama, bayan da ta lallasa Jamus da ci 1-0, sakamakon kwallon da Mats Hummels ya ci kansu a fafatwa mai zafi da sukayi na rukunin F a ranar Talata.

Talla

Hummels - wanda aka kirashi don buga wannan gasa ya karasa aikin da Lucas Hernandez yayi, wajen zuruwa ragarsu kwallo da kansa a mintuna 19 da soma wasar da ya burge ‘yan kallo a Munich.

Dan wasan Jamus Hummels yayin da yake takaicin cin gidansu a wasan da suka fafata da Faransa a gasar Euro 2020, ranar 15 ga watan Yuni 2021
Dan wasan Jamus Hummels yayin da yake takaicin cin gidansu a wasan da suka fafata da Faransa a gasar Euro 2020, ranar 15 ga watan Yuni 2021 Matthias Hangst POOL/AFP

Alkalin wasa yaki amincewa da wani kwallo da Paul Pogba ya aika kuma Kylian Mbappe ya mikawa Karim Benzema ya karasa raga, amma yace satar fage ne.

Haka ma wani kwallo da Klian Mbappe ya ci, shima aka hana, amatsyin satar fage wato offside.

'Yan wasan Faransa yayin fafatawar su da Jamus a gasar Euro 2020, ranar 15 ga watan Yuni 2021
'Yan wasan Faransa yayin fafatawar su da Jamus a gasar Euro 2020, ranar 15 ga watan Yuni 2021 WOLFGANG RATTAY POOL/AFP/Archives

Nasarar Faransa na nufin su da Portugal, wadanda suka doke Hungary 3-0 a Budapest, sun dauki matakin farko a rukunin F.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.