Real Madrid-Kwallon Kafa

Real Madrid ta sallami Sergio Ramos

Sergio Ramos na Real Madrid
Sergio Ramos na Real Madrid REUTERS/Sergio Perez

Kungiyar Real Madrid ta sallami kaften dinta Sergio Ramos bayan ya shafe tsawon kakanni 16 yana taka mata tamola, yayin da ta ce, a gobe Alhamis za ta yi masa bikin karramawa kafin ban-kwana da shi baki daya.

Talla

Za a karrama gwarzon dan wasan a bikin da zai samu halartar shugaban Real Madrid, Florentino Perez.

Dan wasan mai shekaru 35, ya yi ta fama da rauni a wannan kaka kuma wasanni biyar kacal ya buga wa kungiyar tun farkon wannan shekara.

A jumulce Ramos ya buga wa Real Madrid wasanni 671 tare da jefa kwallaye 101 a kungiyar, inda kuma ya lashe mata kofunan La Liga biyar, da kofunan Gasar Zakarun Turai hudu da kuma Copa del Rey guda biyu.

Ramos da Real Madrid sun gaza cimma matsayar tsawaita masa kwantiraginsa wanda zai kawo karshe a ranar 30 ga wannan wat ana Yuni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.