Pogba - Ronaldo

Pogba ya kawar da kwalbar barasa a teburin dake gabansa

Dan wasan Faransa Paul Pogba da takwaransa na Portugal Cristiano Ronaldo yayin wani wasa a Faransa ranar 11 ga watan Oktoba 2020.
Dan wasan Faransa Paul Pogba da takwaransa na Portugal Cristiano Ronaldo yayin wani wasa a Faransa ranar 11 ga watan Oktoba 2020. Gonzalo Fuentes/Reuters

Wasu Kamfanonin dake daukar nauyin wasannin gasar neman cin kofin Turai ta EURO 2020 sun fara nuna damuwa dangane da dabi’ar da wasu fitattun ‘yan wasa keyi, inda suka ce hakan da a Amurka akayi da sai an hukunta ‘yan wasan.

Talla

Wannan na zuwa ne bayan da Chiristiano Ronaldo da kuma Paul Pogba suka gusar da kayan sha dake gabansu gabanin amsa tambayoyin ‘yan jaridu.

Paul Pogba

Dan wasan tawagar Faransa, Paul Pogba ya matsar da kwalbar barasa  dake gabansa a lokacin da zai gana da 'yan jaridu, bayan nasarar da suka samu kan Jamus da ci 1- 0  a gasar Euro 2020 ranar Talata, a matsayin gwarzo a wasan.

Ronaldo

Hakan na zuwa bayan da shima Cristiano Ronaldo ya janye kwalaben Coca Cola dake gabansa bayan wasan da Portugal ta lallasa Hungary da ci 3-0.

Matakin Ronalda ya janyo wa kamfanin Cocoa Cola asarar dala biliyan 4 cikin ‘yan sa’o’i, sai dai ya zuwa yanzu babu bayanan asarar da Pogba wanda Musulmi ne ya janyo wa kamfanin barasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.