Wasanni - Seria A

Buffon ya sake komawa Parma shekaru 20 bayan rabuwa da ita

Gianluigi Buffon.
Gianluigi Buffon. Marco BERTORELLO AFP

Fitaccen mai tsaron raga a gasar Seria A Gianluigi Buffon, ya koma tsohuwar kungiyarsa ta Parma, shekaru 20 bayan rabuwa da ita.

Talla

Karkashin yarjejeniyar da suka kulla, Buffon mai shekaru 43 zai hasakawa Parma har zuwa 30 ga watan Yunin shekarar 2023.

A watan Mayun da ya gabata, Buffon ya bayyana shirin kawo karshen zamansa da Juventus, kungiyar da ya kulla yarjejeniya da ita tun a shekarar 2001 tun bayan rabuwa da Parma a waccan lokacin, baya ga kakar wasa 1 ta 2018/2019 da Buffon yayi tare da PSG.

Wasanni 685 fitaccen mai tsaron ragar ya bugawa kungiyar Juventus kafin rabuwa da kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.