Wasanni - Italiya

Gattuso ya rabu da Fiorentina makwanni 3 bayan kulla yarjejeniya

Tsohon kocin Fiorentina Gennaro Gattuso.
Tsohon kocin Fiorentina Gennaro Gattuso. © Reuters

Sabon kocin Fiorentina Gennaru Gattuso ya ajiye aikinsa makwanni uku kacal bayan kulla yarjejeniya da kungiyar dake gasar Seria A a Italiya.

Talla

Cikin sanarwar da ta wallafa a shafinta na yanar gizo, kungiyar ta Fiorentina ta ce sun fahimci juna da Gattuso kan dalilan da ya bayar na janye amincewar da yay ikan yarjejeniyar da ya rattabawa hannu na jagorantar ‘yan wasanta a sabuwar kakar wasan dake tafe.

A ranar 25 ga watan Mayu Fiorentina ta kulla yarjejeniyar da Gennaru Gattuso kasa da sa’o’I 48 bayan sallamarsa da kungiyar Napoli tayi, wanda kuma a karkashin yarjejeniyar da suka cimma, tsohon kocin na AC Milan zai soma aiki a ranar 1 ga watan Yuli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI