Wasanni - Kwallon Kafa

Tilas ce ta sani rabuwa da Real Madrid - Ramos

Tsohon kaftin din Real Madrid Sergio Ramos.
Tsohon kaftin din Real Madrid Sergio Ramos. AFP

Tsohon kaftin din Real Madrid Sergio Ramos ya ce ya rabu da kungiyar tasa ce ba don yana so ba, sai domin janye tayin da ta yi masa na tsawaita yarjejeniyar dake tsakaninsu.

Talla

Yayin taron manema labarai na bankwana da yayi a jiya Alhamis, Ramos ya ce tabbas ya nemi tsohuwar kungiyar tasa ta tsawaita yarjejeniyarsu da shekaru 2 a baya, to amma a lokacin da ya sauya shawara wajen amincewa da tayin yarjejeniyar shekarar 1 da Madrid ta mika masa, sai kungiyar ta shaidawa wakilinsa cewar sun soke tayin da akalla mako 1 kafin fitaccen mai tsaron bayan ya yi amai ya lashe.

Ramos mai shekaru 35 bai bayyana inda zai koma ba, duk da cewa tsohuwar kungiyarsa ta Sevilla ta yi masa tayin yarjejeniyar shekaru 5.

A shekarar 2005 Ramos ya koma Real Madrid daga Sevilla akan euro miliyan 27, inda daga nan ya zama daya daga cikin fitattun ‘yan wasan kungiyar, wadda ya bugawa wasanni 671, ya ci mata kwallaye 101, gami da bada muhimmiyar gudunmawa wajen lashe kofuna 22 da Real Madrid tayi, ciki har da na gasar La Liga 5, da kuma na gasar Zakarun Turai 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.