Wasanni - Kokuwa

Isaka dan kokuwar Dosso ya lashe kambin shugaban kasar Nijar

Wasan kokuwa da aka gudanar a Birnin Maradi inda Bube Bourema na Agadaz ya kada Umaru Bindgou na Maradi
Wasan kokuwa da aka gudanar a Birnin Maradi inda Bube Bourema na Agadaz ya kada Umaru Bindgou na Maradi RFI/Awwal Janyau

A jamhuriyar Nijar, Dan damben Doso, Isaka Isaka ya lashe kambin  shugaban kasa na musamman, bayan doke abokin karawarsa na Tilaberi Usman Hasan.

Talla

An shirya kokuwarce albarkacin bikin bude katafaren filin danbe na nazamani da aka gina a garin Maradi a jiya Lahadi, filin da ya lakume tsabar kudi CFA biliyan 2.

Ministan wasanni da matasa Adamu Seku Doro ya jagoranci mika kyautukan bayan shafe kwanki uku na kwambala data hada yan kokowa hudu hudu daga jihohi takwas na Nijar, a sabon filin kokowar mai daukar mutane dubu biyar.

Ihun matasa

To sai dai kuma wanda ya lashe kofin Isaka Isaka yace ba zai sake fafatawa a filin na Maradi ba sakamakon abin da ya faru bayan nasarar tasa inda matasa sukayi ta ihu cewa basu amince da nasarar ta sa ba, lamarin da ya bata masa rai, “yana mai cewa dan Nijar ne ya lashe kofin ba dan wata kasa ba”

‘Yan sanda sunyi amfani da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa matasan da ke goyan bayan Usman Hasan na Tilaberi da ya sha kaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.